Spread the love

‘Yan kwallo dake wasa a kungiyar kwallon kafa ta jihar Katsina waton Katsina United sun yi farinciki da goma ta arzikin da gwamnan Katsina Aminu Bello Masari ya yi masu na biyansu dukkan watanni hudu da suke bin gwamnatinsa tun da aka fara wannan annoba ta Korona.

Shugaban Kungiyar Abdussamad Badamasi ya bayyana hakan ga manema labarai a lokacin da yake godewa gwamnan kan biyansu albashi da alawus na ‘yan wasan da jagororinsu.

“Ina farincikin sanar da al’umma gwamna ya biya mu albashin da muke biyar gwamnati, maganar da nake yi a yanzu ba wani dan wasa da bai tafi gida da kasa da miliyan daya da dubu dari shidda ba (1.6m).”

Badamasi ya roki ‘yan wasan su zama masu sadaukarwa ga kungiyar kwallon don sanya farinciki ga  gwamna, abin da ya yi yakamata a gode masa.

Katsina United tana cikin kungiyar kwallon kafa ‘yan kadan da ba su biyar gwamnati bashi.

Badamasi ya ce za su sallami ‘yan wasan da ba su iya taka leda yanda yakamata, lokaci ya zo ga wadan da suka gaza su bayar da wuri ga masu jini a jika don kai kungiyar mataki na gaba.

Shugaban ‘yan wasan(Captain) Usman Bara’u ya tabbatar da an biya su albashin da suka dade suna jira.

Ya ce sun sha wuya amma yanzu komi ya wuce amadadin ‘yan uwansa masu shura kwallo a kungiyar sun godewa Gwamna sosai.  

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *