Spread the love

Tsohon gwamnan jihar Sakkwato Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya ce yafi son al’ummar jihar Sakkwato su yi magana kan mulkin Gwamna Aminu Waziri Tambuwal yafi dacewa su yi ‘Tambuwal kanena ne kuma yaro ne yana iya yin kuskure.’

Sanata Wamakko haka ma ya goyi bayan a cigaba da karba-karba a mulkin Nijeriya saboda samun hadin Kai da zaman lafiya da cigaban kasa cikin fahimtar juna. Duk da kowa ne dan kasa na da damar mulkar kasarsa.

Kan maganar yadda suke rike da jam’iyarsu a Sakkwato ganin su ‘yan adawa ne a jihar ya ce duk da PDP ce ke da gwamna a jihar Sakkwato amma jihar ta APC in aka yi La’akari da zaben da ya gabata jam’iyarsu ce ke da rinjaye a majalisar dokokin jiha da tarayya, yadda sakamakon zaben gwamna ya fito abu ne kawai na lokaci.

Wasu na ganin yakamata Wamakko ya fadi matsayarsa da yanda yake kallon tafiyar gwamnatin Tambuwal don sanin ko tana Samar turbar da yake ganin za a samu cigaba a jihar, amma rashin cewa komai kan gwamnati cikas ne a tafiyar siyasar jihar Sakkwato.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *