Spread the love

Daga Aminu Abdullahi Gusau.

A kokarin tallafa wa mabukata domin rage radadin zaman gida, dalilin cutar murar mashako,(Covid-19). Rundunar Sojan Najeriya ta rabawa mutane fiye da dubu daya kayan abinci a kananan hukumomin Faskari ta jihar Katsina da kuma Kauran Namoda dake jihar Zamfara.

Da yake gabatar da kayan tallafin ga wadanda suka amfana da shirin a wadan nan kananan hukumomin, Shugaban hafsan sojin Najeriya Laftanal janar Yusuf Tukur Buratai, ya ce wannan tallafin na daya daga cikin kokarin da rundunar sojin ke yi na taimakawa marassa karfi, don su samu saukin yanayin da aka shiga sakamakon Murat mashako waton Korona.

Hafsan Sojojin na Najeriya wanda ya maganta ta bakin wakilinsa, Major Janar Nuhu Angbazo, wanda shi ne shugaban wata ruduna ta ukku, watau (3 Division), yace sunzo da wannan tallafin ga mutanen Faskari domin rage masu radadin zaman gida saka mako wannan cutar.

Haka ma yaja kunnen su da su ba sojojin goyon baya domin yaki da yan ta’addan dana addabi yankin su , da sauran jihohin arewacin Najeriya.

Karamar hukumar mulkin Kauran Namoda kuwa, Buratai ya samu wakilcin Shugaban sashen ingantawa da kirkirar sabbin dabarun yaki na hedikwatar rundunar dake Abuja manjo janar E. N Njoku, inda ya ce shekaru da dama rundunar na gudanar da tsare-tsaren ganin ta bada nata gudunmuwar.

Ya kara da cewa yana jinjinawa alummar jahar Zamfara baki daya, bisa ga cikkaken goyon baya da hadin kai da suke baiwa rundunar wajen yaki da ta’addanci a wannan jihar, ya kuma bukaci alummar da su ci gaba da bada wannan hadin kai don cimma nasara.

Ya kara da cewa, wannan tallafin yana daya daga cikin bukin ranar Soja ta wannan shekara watau (Nigeria Army Day Celebration 2020),domin kara dankon zumunci tsakanin sojoji da kuma mutanen gari.

Cikin Kayayyakin da aka raba sun hada da kananan buhunan shinkafa, da kayan shayi, da maggi, da ruwan roba, da kuma littafai, inda kowace karamar hukuma ta samu littafan rubutu dubu goma.

Wannan hobbasa ce da ake son kowace al’umma su yi don taimakon maras karfi da ke cikinsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *