Spread the love


Daga Mukhtar A Haliru Tambuwal Sokoto.

Uwar Gidan Gwamnan jihar Sakkwato Hajiya Mariya Aminu Waziri Tambuwal ta bayan cewa a Nigeria akwai mata zawara wadan da aka kididdige su,a jihohi daban daban, kuma suna bukatar kulawa da taimakawar al’uma.


Uwar gidan gwanmna ta fadi haka a jawabin da ta yi wurin rabawa zawara kayan tallafin sana’a albarkacin ranar duniya ta zawarawa,Wadda ake gudanarwa a 23 ga watan Yuni na duk shekara.


Uwar Gidan Gwamnan Wadda ake yiwa lakabi da uwar marayu, ta ba da tallafin ne da sanar da uzurin da ya sanya sai a yanzu ne ta yi bukin ranar wadda ta riga ta wuce domin matsala walwala da babu akan cutar Covid 19 da ta addabi duniya, Wanda dandalin hadakar matan gwamnoni najeriya suka ga yakamata kowacce Uwar Gidan Gwamnan jiha ta aiwatar da ire-iren wannan tallafi a jiharta, Wanda suke ganin zai taimakawa zawarawa wajen dogaro dakai tare da rage musu radadin rashin mazajensu da suka yi.

Ta bayyana cewa yanzu haka a Najeriya akwai adadin Zawarawa miliyan ukku da rabi, don haka ta Shawarci wadanda suka amfana da su yi kokari wajen dogaro dakai Wanda zai basu damar yin lalurorin su ba tare da zama cima-kwance ga kowa ba kuma ta kara da jaddada goyon bayanta dana dandalin matan gwamnoni Najeriya ga shugabannin kungiyar zawarawar da membobinta ako da yaushe,ta shawarci wadanda suka amfana da su guji yin bukukuwa ko hidimar biki barkatai gudun ka da jallin da aka ba su ya Karye.


Haka Kuma tayi godiya ga hukumar Zakka da wakafi ta jihar Sakkwato akan irin namijin kokarin da suke yi a jihar Sakkwato wajen sauke nauyin da ke kan su,Wanda akan haka ne maigidanta ya umurce ta, ta hada hannu da hukumar dan zakulo wadan da suka dace, dan su amfana,ta bayyana kudurin Gwamna Tambuwal na cigaba da kulawa da lamurran Mata.
Tun daga farko sai da Shugaban Hukumar zakka da wakafi ta jihar Sokoto Malam muhammad Lawal Maidoki sadaukin Sakkwato ya yi tunatarwa da gargadin wadan da zasu amfana da suyi amfani da abin da aka basu kasan cewar Allah ne ya cida su, Ya bayyana cewa suna da kididdiga da suka hada a daukacin gundumomin jihar ta Mata Zawarawa,Mabukata,yara marayu,Maras aikin yi da sauran su.
Wasu da muka zanta da su, sunyi godiya da Addua ga duk Mai hannu a ciki.


Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *