Daga Ibrahim Hamisu, Kano.

Marigayi Alhaji Yusuf Maitama Sule Dan masanin Kano, yana daya daga cikin jigogin siyasar arewaci da ma Najeriya baki daya, wanda ya fara siyasarsa tun a jamhuriya ta farko. Yana daya daga cikin wadanda suka fara kafa kungiyar da ta zamo babbar jam’iyyar siyasar Arewa, NPC.

Haka kuma, yana daya daga cikin jigogin da suka kafa jam’iyyar NPN a jamhuriya ta biyu, har ma ya nemi tsayawa takarar shugaban kasa karkashin inuwar jam’iyyar.

Marigayin shahararren dan siyasa ne a Najeriya, wanda ya taba rike mukamin minista da kuma jakadan kasar nan a Majalisar Dinkin Duniya.

Ya zama minista lokacin Fira Ministan Najeriya na farko Alhaji Abubakar Tafawa Balewa.

Hakazalika, galibin mutane za su rika tuna wa da marigayin ta wajen yadda ya kware wajen iya magana.

A shekarar 1976 ne aka ba shi kwamishinan gwamnatin tarayya mai kula da korafe-korafen jama’a.

Yayin da a shekarar 1979 ya tsaya takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar NPN, sai dai Shehu Shagari ne ya lashe zaben.

Har ila yau, gwamnatin Shagari ta nada shi jakadan Najeriya na dindindin a Majalisar Dinkin Duniya watanni bayan kammala zaben.

A can ne ya jagoranci Kwamitin Musamman kan Yaki da Wariyar Launin Fata na majalisar, wanda masu sharhi ke ganin ba karamin matsayi ba ne.

Hakazalika, bayan da Shugaba Shagari ya lashe zabe a shekarar 1983 ya sake nada shi Minista Mai Kula da Tafiyar da Kasa, wato mai taimakawa shuagabn kasa kan yaki da cin hanci.

An taba ruwaito shi yana cewa: “Kowane mutum yana da baiwar da Allah Ya yi masa. Allah Ya ba ‘yan arewa kwarewa ne wajen shugabanci. Bayarabe wajen dogaro da kai da kuma kyawawan dabi’u. Igbo suna da baiwa wajen kasuwanci da kuma kere-kere. Allah Ya halicce mu daidai kuma kowa da baiwar da Ya yi masa.”

Wasu sun yi amfani da wannan kalami nasa wajen bayyana damuwa game da yadda ‘yan arewa suka mamaye fagen shugabancin kasar.

A shekarar 1957 kafin Najeriya ta samu ‘yancin kanta, marigayi Maitama Sule shi ne ya kewaya da Sarauniyar Ingila Elizabeth yayin da ta kawo ziyara Kano yana yi wa jama’a bayaninta.

Dan Masanin Kano ya rasu ranar litinin 3 ga watan Yulin shekarar 2017, ya bar ‘ya ‘ya 10 – maza hudu, mata shida,

Dubun dubatar‘yan Najeriya ne suka halarci sallar jana’izar sa da Limamin babban Masallacin Kano Farfessa Mohammed Sani Zaharaddeen ya jagoranta,

Bayan rasuwar dan masanin Kano ne dai Gwamnan Ganduje ya sauya sunan Jami’ar North west zuwa Maitama Sule don karamci da tunawa da wannan fasihin dan kishin kasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *