Jam’iyar APC mai mulki a Nijeriya ta tura gwamna biyar da wasu manyan ‘yan siyasa dake cikin jam’iyar, su 44 da tsoffin shugaban jam’iyar na kasa guda biyu, su je jihar Edo a matsayin jagorori da mambobin yekuwar cin zaben jihar.

Kwamiti rikon kwaryar ya bayyana gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ne zai jagoranci kwamitin ya yinda gwamnan Imo zai yi mataimaki, Abbas Braimoh zai yi Sakatare.

Za a kaddamar da kwamitin a ranar Litinin mai zuwa a hidikwatar jam’iya wanda shugaban rikon kwaryar Gwamnan Yobe Mai Mala Buni zai yi.

Gwamonin sun hada da Gwamnan Gombe, Kogi da Lagos, sai sauran ‘yan siyasar akwai Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko da Sanata Orji Uzor Kalu da Sanata Rochas Okorocha da sauransu.

Gwamnan jihar Edo Godwin Obaseki da ke son sake zama gwamna a karo na biyu a jihar ya ce ya shiryawa karon batar karfen a lokacin da yake mayar da martanin nada wadan nan gwamnoni don ganin bai samu nasara ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *