Daga Ibrahim Hamisu, Kano.

Ƙungiyar lauyoyi ta ƙasa reshen jihar Kano wato NBA ta zabi Aminu S. Gadanya a matsayin sabon shugabanta.

Jaridar Kano Focus ta ruwaito shugaban kwamitin gudanar da zaben Tajuddeen Funsho ne ya sanar da sakamakon zaɓen, inda Aminu S Gadanya ya samu ƙuri’u 214 inda ya yi nasara akan Aminu Garba Waru, wanda ya samu ƙuri’u 137, sai kuma Usman Umar Fari da ya samu ƙuri’u 38.

Sauran muƙaman da aka zaɓa sun haɗa da Isma’il Abdulazeez a matsayin ma’ajin ƙungiya da kuma Mukhtar Shehu Bello a matsayin mataimakin sakatare, sai kuma Asma’u Muhammad a matsayin sakatariyar walwala.

An kammala zaben lami lafiya, shugabanni za su soma wa’adin mulkinsu da nasara kamar yadda wasu masu yi masu fatan alheri suke fata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *