Spread the love


 Daga Aminu Abdullahi Gusau.


Shugaban Sojojin Najeriya Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai, yace sojojin Najeriya zasuyi hadaka da sauran kawayen su ta fannin bada tsaro domin su fatattaki yan ta’addan dake a yankin arewa maso yammacin kasar nan.


Janar Buratai yayi wannan kalaman ne a Karamar hukumar Faskari dake jihar Katsina, a lokacin da yake bude bukin  ranar Soja, ta wannan shekara 2020(watau Nigerian Army  Day Celebration 2020).


Shugaban sojin ya kara da cewa, jadawalin wannan bukin wanda zai daukesu sati daya, an shir yashi  ne a jihar Katsina domin bada kwarin gwiwa ga sojojin dake wayan nan jihohin dake fama da yan ta’adda, domin kakka besu baki daya.


Laftanar Janar TY Buratai, yace shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada oda ga sojoji da suji gaba dakai wa yan ta’adda farmaki a wayannan wuraren da suke boye, wanda shi yasa suka kara fadin aikin su, wanda suka yiwa lakabi da  Sahel Sanity’.


Daga nan sai yaja hankalin zaratan sojojin nasa da cewa zasu wannan aikin ne a karkashin dibishin NA ‘8 da kuma birigade na ’17 NA sojan Najeriya domin su gano mabuyar yan ta’adda a ciki daji, kuma su gasa masu aya a hannunsu.


Ya ba Mutannen da wannan abin ya shafa na jihohi biyar tabbacin  cewa soja tare da hadin  gwiwar sauran jami’an tsaro, zasu kawar da yan ta’adda tare da la’akari da bin ka’idar aiki.


 Wannan bukin na (2020 Nigerian Army Day Celebration) anyi mashi lakabi da “kare iyakokin Najeriya da kimar su, da kuma bada horo na musamman da zaratan sojojin Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *