Spread the love

Gwamnatin tarayyar Nijeriya a jiya(Talata) ta cire haramcin da ta sanya na hana zirga-zirga a tsakanin jihohin Nijeriya, daga gobe Laraba kowa zai iya tafiya jihar da yake so ba da wani sanke ba.

Sakataren gwamnatin tarayyar Nijeriya Boss Mustapha ne ya sanar da haka a lokacin da suke yi wa manema labarai bayani a Abuja.

Ya ce gwamnati ta amince jiragen sama na sufuri su dawo kan harkokinsu , sannan yaran makarantar firamare da sikandare da suke ajin karshe su dawo domin rubuta jarabawa.

Haka kuma dokar hana yawo da aka sanya tana nan kamar yadda aka sanya daga karfe 4 na dare zuwa 10 na dare a kowace rana.

Muatane da dama sun yi farincikin jin labarain dawo da harkar zirga-zirga a tsakanin jihohi tun daga direbobin mota da suka sha bakar wuya kan dakatarwa da fasinjoji masu tafiya domin yin wasu bukatu na rayuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *