Spread the love

Muhammad M. Nasir.

Shugabannin majalisar dokokin Nijeriya sun shiga maganar Karin kudin wutar lantarki da aka shirya aiwatarwa a 1 ga watan Yulin shekarar 2020.

Sun yi nasarar cimma matsaya tsakaninsu da kamfanonin rarraba wutar lantarki  an bar shirin Karin  har zuwa zangon farko na shekarar 2021.

Shugaban majalisar dattijai Sanata Ahmad Lawan da Kakakin majalisar wakillai Femi Gbajamiala da sauran shugabannin zauren biyu ne suka yi zama da jagororin kamfanin na kasa baki daya, wannan bayanin ya fito ne a bakin mai ba da shawara na musamman kan harkokin yada labarai ga shugaban majalisar dattijai Ola Awoniyi.

Ya ce za su dauki matakin da ya kamata kafin lokacin da za a kara kudin yanda abin zai zama mai alfanu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *