Spread the love

Fitaccen jarumin nan a masana’antar Kanywood kuma tsohon gwamna jihar Alfawa, a cikin shirin kwana casa’in a gidan talabijin na Arewa24, Sani Muazu Jos ya nemi jama’a da su taya shi zaɓar matar aure  da zai ƙara ta biyu da ita a matsayin amarya kuma macen ta zama daya daga cikin mata ne masu shirya finafinnan Hausa. 

Sani Muazu ya bayyana hakan ne a shafinsa na tiwita, cikin harshen turanci, inda ya buƙaci jama’a da su tayashi zaɓen wacce zai aura a cikin kyawawan ‘yan matan da su ke masana’antar Kanywood waton wasan kwaikwayo na Hausa. 

“Ina da aure kuma matar ba a masana’antar Kanywood na aure ta ba, kuma ina gaf da ƙara aure daga cikin ‘yan matan da su ke masana’antar Kanywood, kuma zan yi haka a matsayin ƙarfafa gwiwar zaman tare”

“A bisa wannan na ke neman ku taya ni zaɓe a cikin kyawawan jarumai mata da mu ke da su a cikin masana’antar Kanywood. Ba da wasa na ke ba, maganar gaskiya na ke yi”

Sai dai ana kallon jaruman Kanywood maza ba su cika auren abokan aikinsu mata ba, domin wadan da suka yi haka ba su da yawa ko kashi daya bisa uku ba a samu ba.

Managarciya ta fafimci Kallon da ake yi wa ‘yan wasan  na rashin tarbiya da kamun kai na kara sanya maza na gudun nemansu aure domin ko ka nema uwayenka ba za su bari ba, hakan ya kara sanya da yawan maza na gudun fito da maganar son auren ‘yar wasan Hausa.

Matan a yanzu halinsu na son burge jama’a da sanya suturar ke ce raini da mallakar motar alfarma da gina kasaitaccen gida, da buda katafaren shagon sayar da wani abin amfani ya sa mutanen da ke bibiyar harkokin finafinnan Hausa sanya alamar tambaya ga matan cewa suna iya zaman aure kuwa, namiji na iya mallakarsu kuwa, suna iya sadaukar da dukkan wannan samu saboda aure, suna iya aminta a mayar da su rayuwarsu ta baya kafin shigarsu harkar fim? Wadan nan da ma wasu tambayoyin nasa mazan waje da masu shirya fim ke dari-dari da matan fim na Hausa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *