Spread the love

Muhammad M. Nasir.

Direban motar haya Malam Kiri Umaru da ya tsinci miliyan daya kuma ya mikawa mai kudin abinsa.

Sanannen direba ne dake jigilar mutane daga cikin gari zuwa kauyukka a jihar Yobe ya ce ya dade yana wannan sana’a sama da shekara 10.

Malam Umaru ya ce a lokacin zai tafi Gashua daga Dapchi sai ya hangi leda a gefen hanya ya tsaya,  ko da ya duba ledar sai ya samu makudan kudi ne a ciki, daga nan ya yi sauri ya rufe ba tare da sanin fasinjojin da ya dauko ba.

Bayan ya iso Gashua sai ya damka kudin ga kungiyar direbobi don a nemi mai kudi a hannunta su gare shi.

Bayan ya yi haka a garin Gaidam rigima ta kaure tsakanin masu kudin da direban wata mota da yadauko su kan sai ya ba su kudinsu da suka zo sayen dabbobi, fadowar wani direban ne ya fada masu kudi na can Gashua ana neman mai su, da suka je suka yi bayani aka ba su abinsu.

Sun nemi Malam Umaru su ba shi tukuici ya ce yana Damaturu ba zai iya dawowa ba, sun matsa amma ya ki dawowa.

“Na yi haka ne saboda Allah, ba zan iya rike wadan nan makudan kudin ba kuma in samu natsuwa, na gode Allah da halin da nake ciki.” a cewarsa.

Wani dan kungiyar direbobin ya gayawa daily trust cewa masu kudin sun ba da dubu 20 a ba shi, a matsayin tukuici.  

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *