Spread the love

Gwaman Yobe Mai Mala Buni ne jam’iyar APC ta nada shugaban rikon kwarya da zai gudanar da zaben shugabannin jam’iya sabbi nan da wata shidda.

Hakan ya biyo bayan soke shugabannin jam’iya da majalisar zartarwar jam’iyar ta aiwatar.

Wannan matakin ya biyo bayan aminta matakin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi.

A jawabin da ya gabatar sabon shugaban na rikon kwarya ya ce a matsayinsa na wanda ya rike kujerar sakataren jam’iyar karo biyu ya san jam’iyar ciki da baya, wannan magana ce ta yi kowane dan jam’iya adalci , matukar babu adalci tau ba zaman lafiya, in ka kasa magance matsala yanda ya kamata, to ita za ta gama da kai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *