Spread the love

Daga Muhammad M. Nasir.

Harkar yiwa mata fyade tana kara ta’azzara a cikin al’umma abin da ke bukatar malaman addini da hukumomin da suka dace su tashi tsaye wajen kawo karshen wannan musibar ko a samun raguwarta kwarai.

 A kididigar da majalisar dunkin duniya ta yi a yanzu haka ya nuna mata 137 ne ke rasa rayukkansu a kullum sanadiyar ke ta mutuncinsu da aka yi ta hanyar yi masu fyade ko wani cin zarafi.

Kungiyar kwadago ta nemi gwamnatin tarayyar Nijeriya ta shirya taron da zai duba hanyoyin magance cin zarafin da keta haddin mata da ake yi wanda lamarin ya kai ko kaka.

A hukumance kididigar da majalisar dunkinduniya ta fitar kashi 35 na mata a duniya na fuskantar cin zarafin fyade na mutane  ko musgunawa ta zahiri ga makusantansu.

Bayanin ya bayyana a kalla mace  137 ce ke rasa ranta a kullum ta sanadin hatsaniya da ke tasowa  mafiyawa a cikin dangi.

Haka ma mutanen  da ake fita da su don bautar da su a duniya gaba daya kashi 72 mata ne manya da kanana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *