Spread the love

Daga Muhammad M. Nasir

Rikicin shugabanci ya mamaye jam’iyar APC mai mulki a Nijeriya in da gwamnonin da aka zaba karkashin inuwar jam’iyar suka rabu gida biyu kan jagoranci jam’iya.

Gwamnoni 13 suna goyon bayan cigaba da jagorancin bangaren tsohon gwamna Abiola Ajimobi, yayin da gwamnoni 7 da suka kira kansu ‘masu saisaita tafiya’ da suke kokarin karbe jagorancin jam’iyar suka nuna adawarsu ga cigaban jagorancin ganin yanda dakataccen shugaban jam’iyar Adam Oshiomhole ya kawowa jam’iyarsu ci baya da rasa gwamnoni a wasu jihohi da jam’iyarsu ke jagoranci a baya, suna ganin canja salon jagoranci ne zai kai jam’iyar tudun mun tsira.

Gwamnoni 13 dake goyon bayan Ajimobi suna zargin jam’iyar adawa ta PDP ce kara wa wutar rikcinsu ruruwa, amma duk da haka suna neman hanyar magance ta. Sauran gwamnonin bakwai da ba su gamsu da tafiyar ba, suna kan kokarin sai sun saisaita tafiyar jam’iyar, ana zargin wasu ministoci na mara masu baya a rikicin.

Majiyoyi da dama sun tabbatar da duk wannan rikicin na yunkurin karbe jam’iya ana yinsa ne kan kakar zabe ta 2023.

Managarciya na kallon tarihi na iya maimaita kansa, wadan nan gwamnonin guda bakwai suna iya barin jam’iyar APC matukar ba su yi nasara ga abin da suka dauko ba, kamar yadda wasu gwamnoni biyar suka bar jam’iyar PDP a lokacin da hakarsu ba ta cimma ruwa ba.

Wannan rikicin ya fara kenan har a gudanar da zaben 2023 ba ranar barinsa domin siyasar 2023 ce aka soma a wannan fuska.  

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *