Tsohon shugaban jam’iyar APC na kasa chif John Odigie Oyegun a jiya ya yi kira da a saukar shugabannin jam’iyarsu a nada masu rikon kwarya da za su saisaita rikicinci jam’iyar wannan kiran ya ce ya zama wajibi ya yi shi.

Jawabin nasa ya yi masa taken ‘kafin a makara’ya ce shugabanin zartarwar jam’iyar su hadu su samar da shugabannin rikon kwarya da za su shirya taron zabar shugabanni na kasa na musamman.

Ya yi kira ga shugaba Muhammadu Buhari a matsayinsa na jagoran jam’iya ya yi abin da ya dace kar jam’iyar ta ruguje.

Ya ce ina alfahari ga cigaban da aka samu a mulkin Buhari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *