Spread the love

 Kungiyar Gwamnonin Arewa sun yi taro a ranar Alhamis data gabata  don duba yanayin rashin tsaro da ya addabi yankin a wannan lokacin.


Zaman  da aka yi ta yanar gizo wanda shugaban kungiyar gwamnonin, Simon Bako Lalong ya jagoranta, ya jajanta wa yankin  kan karuwar rashin tsaro a  arewa, gwamnonin sun fara zantawa a kan matakan da za’a dauka a kan rashin tsaron.


Daga cikin matakan da suka amince da su  za a kafa kwamitin kula da tsaro a Arewa wanda zai dinga duba al’amuran tabbatar da tsaro a yankin, Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello shi aka nada shugaban kwamitin yayin da Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara da takwaransa na Gombe Muhammad Inuwa Yahaya su ne   mambobinsa.


Sun kuma kara kafa wani  kwamitin  karkashin  shugabancin gwamnan jihar Filato Simon Lalong da gwamna Ahmadu Fintiri, Abubakar Bello da Aminu Tambuwal su ne za su tuntubi malaman addinai da sarakunan gargajiya da shugabannin yankuna a arewa, kamar yadda mai magana da yawun Gwamna Lalong ya sanar, kwamitin zai tabbatar da an saka bangarori da yawa wurin shawo kan matsalar tsaro a arewa.


Kuma gwamnonin sun yanke hukuncin saka ‘yan sa kai (banga), mafarauta da kuma kungiyoyin yankuna don tsara tsaron yankin tare da inganta rahotannin sirri, saboda haka suka yi kira ga gwamnatin tarayya da ta duba tsaron ECOWAS na barin shige da fice ta iyakokin kasar nan musamman a arewa.


Sannan sun jinjinawa gwamnatin tarayya a kan kokarin shawo kan matsalar tsaro, sun yi kira ga gwamnatin da ta inganta tare da tallafawa don kawo karshen ayyukan ‘yan bindiga, kuma sun amince da duba tsarin tattaunawa tare da amfani da tsarin dakarun soji wajen shawo kan kalubalen tsaro a Arewa.


A baya bayan nan yankin Arewa na fama da matsalar tsaro sosai abin da ake ta kira ga masu ruwa da tsaki su dauki matakin shawo kan matsalar. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *