Spread the love

Jam’iyar APC ta rasa Gwamna Godwin Obaseki ya koma jam’iyar PDP in da zai shiga zaben neman sake zama gwamnan jihar Edo a Karo na biyu.

Gwamnan ya shiga jam’iyar PDP a yau Jumu’a ya ba da sanarwar shiga jam’iyar a sakatariyarsu dake cikin birnin Benin.

Obaseki ya ce ya bar jam’iyarsa ne domin bukatar da yake da ita na cigaba da kawo cigaba mai daurewa a jiharsa.

Gwamna ya dade yana rigima da dakataccen shugaban jam’iyar APC adams Oshiomhole Wanda tsohon mai gidansa ne a siyasa, wannan rigimar ce ta sa gwamnan ya bar jam’iyar zuwa wata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *