Spread the love

Muhammad M. Nasir

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanar da shugabannin tsaron Nijeriya bai gamsu da kokarinsu ba kan yadda harkokin tsaro ke tafiya a kasa.

A zaman da suka yi a fadar shugaban kasaa jiya(Alhamis) ya ce ba zai sake karbar duk wani uzuri ba don haka su zabura su cimma bukatar da ake da ita a harkar tsaron kasa.

Mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Babagana Munguno a jawabin da ya yi wa manema labarai dake fadar shugaban kasa bayan kammala zaman ya ce sun yi wa shugaban kasa bayanin yanda matsalar tsaro ta  kara ta’azara da yanda za a magance lamarin.

Mungono ya ce shugaban kasa ya nuna bacin ransa kan yadda ba a samu hadin kai da tafiya tare tsakanin jami’an tsaro, don haka su kawar da wannan su yi aiki tare don magance matsalar tsaro a Nijeriya.

Ya ce Buhari ya ba su umarnin su yi zama da gwamnonin Arewa maso yamma(Sakkwato da Zamfara da Katsina) domin su san matsalollin da suke fama da su da fito da hanyoyin magance su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *