Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta fara bincike kan aiyukkan da aka fita butunsu ba a kammala ba  a jihohin Sakkwato da Kebbi da Zamfara, don tabbatar da mai kwangilar zai dawo ya ci gaba da aikinsa da ya soma don ya kammala shi.

Shugaban hukumar na yanki Abdullahi Lawal ne ya bayyana haka a jumuar da ta gabata a Birnin Kebbi lokacin da yake zantawa da manema labarai, ya ce za su binciki aiyukkan da aka fita batunsu a yankin.

Lawal a tare da rakiyar wasu jami’ansa ya bayyana cewa binciken zai taimakwa hukumar ga sanin matakin aiyukkan na kammalawa da yawan kudin da aka kashe ga aiyukkan.


Ya kara da cewar binciken zai tabbatar da duk wani dan kwangila da yake aiyukkan ya kammala su domin amfanar jama’a da cigaban kasa gaba daya.

A jihar Kebbi shugaban ya bayyana hukumarsa ta karbi korafin jama’a a watan Junairun wannan shekara ta 2020 cewa akwai wasu aiyukka da aka fita batunsu da ba a kammala ba a wurare daban-daban a cikin jihar, gwamnatin jihar Kebbi ta fitar da miliyan 949 ga dan kwangilar dake rike da aikin Sakatariyar jihar dake Gwadangwaji.

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *