Spread the love

Uwar jam’iyyar APC ta kasa ta nada tsohon gwamnan jihar Oyo, Sanata Ajibola Ajimobi, matsayin mukaddashin shugaban jam’iyyar.

Hakan ya biyo bayan hukuncin kotun daukaka kara da ta tabbatar da dakatare da Adams Oshiomole matsayin shugaban jam’iyyar.

Kakakin jam’yyar ta APC, Lanre Issa-Onilu ya bayyana hakan a shafin jam’iyyar na Tuwita da daren Talata, 16 ga watan Yuni, 2020.

Jam’iyar ta sake fadawa cikin rikicin shugabanci in da yanzu ba a San inda za ta sa gaba ba, za ta yi kokarin dawowa da gwamnan da ta rasa ne, ko kuma ta hana wasu gwamnoni ficewa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *