Ƙungiyar makarantun Islamiyyu a Kano za su gudanar da zanga-zangar Lumana

Daga Ibrahim Hamisu.

Ƙungiyar makarantun islamiyya a jihar Kano sun bayyana ƙorafinsu akan yadda gwamnatin jihar Kano ta buɗe gidajen kallon Kwallo a faɗin jihar inda kuma ta bar makarantun islamiyyu a garƙame.

Wannan ƙorafi ya fito ne daga bakin wasu daga cikin shugabannin Islamiyyu Aisha Ibrahim Ɗorayi da kuma Malam Aminu Hassan wanda shi ne sakataren kungiyar, a lokacin da su ke tattunawa da filin Inda ranka da ake gabatarwa a tashar Freedom Radiyo da ke Kano.

Malaman makarantun Islamiyya sun ce za su yi zanga-zangar lumana ganin yadda gwamnati ta bude gidan kallo amma bata bude makarantun Islamiyya ba.

Wannan dai yana zuwa ne kwanaki uku da gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya bayar da umarnin buɗe gidajen kallon kwallo da ke jihar Kano.

Gwamna Ganduje ya bayar da wannan umarnin ne a lokacin da ya karbi bakuncin mambobin kungiyar gidajen kallo a jihar Kano.

Hakazalika gwamnan ya yi kira ga masu gidan kallon su tabbatar da cewa an baiwa juna tazara a gidajen kallon da sanya Takunkumi da wanke hannu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *