Spread the love

Daga Aminu Abdullahi Gusau.

Wani jigo a jam’iyyar PDP a karamar hukumar mulkin Tsafe Alhaji Bashiru ya yi kira ga gwamna Bello Muhammed
Matawalle da ya kula da ‘yan jam’iyyar sa, da suka yi gwagwarmaya tare.

Alhaji Bashiru, ya yi wannan kiran ne alokacin da yake zantawa da manema labarai a kan cika shekara daya da ragamar mulkin PDP a jihar ta zamfara.

Ya ce yanzu haka akwai ‘ya’yan jam’iyyar wadanda har yanzu basu san abinda ake ciki ba, ya kara da cewa suna zargin akwai wasu masu hana ruwa gudu kewaye da shi, kuma su ne suke hanashi yin wani abin azo a gani ga sauran yan jam’iyyar PDP a wannan jihar.

A bangare daya kuma ya jinjina wa, gwamna Matawalle kan kokarin da yayi na kawo karshen rashin tsaron daya addabi jihar ta zamfara, yace gaskiya shirin sulhu yayi amfani kwarai da gaske, bisa a lokacin gwamnatin data gabata.

Jigon siyasar ta PDP, haka ma yace, gwamnatin ta samar da Asibiti a kauyuka dake fadin jihar zamfara, inda manyan asibitota suma suka samu kulawa ta musamman.

Alhaji Bashiru, ya kara da yace, a fannin ilimi an tura yayan talakwa kasashen waje domin suyi karatu, bayan haka ya kara da cewa akwai yaran da suka kare karatum furamare wayanda aka turasu makarantun sakandare na kudi domin suci gaba da karatun su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *