Spread the love

Daga Muhammad Nasir.

Jamiyar APC mai yawan rinjayen magoya baya dake adawa a jihar Zamfara  ta bayyana abun da Gwamnatin PDP ta yi na yin mukamman rikon kwaryar kansiloli a kowace mazaba da shugabannin kananan hukumomi da cewa wannan abu ne da ya sabama kundin tsarin mulkin Najeriya.

Malam Shehu Isah Barden Gusau Sakataren yada labaran Jam’iyar APC a Zamfara a  ranar Juma’a da ta gabata ya bayyanawa manema labarai cewa Gwamnatin Zamfara karkashin jagorancin Alhaji Bello Matawallen Maradun ta rantsar da Kansilolin riko a kowace mazaba wanda abu ne  aka yi ba bisa dokar kasa ba, kuma duk me kishin Dimukuradiya ya kamata yayi tir da wannan matakin.

Malam Shehu  ya yi karin haske a kan hukuncin da  babbar kotun kasa ta yi na jahar Ekiti a shekarar 2019 wanda ya haramtawa Gwamnoni ko ‘yan Majalisa tunbuke Shugabannin kananan hukumomi da Majalisarsu, bisa wannan akwai bukatar Gwamnatin Zamfara ta girmama hukuncin babbar kotun kasa, amma sai gashi anzo an yi abun da ko hankali ba zai dauka ba.

Sakataren yada labaran ya bayyana cewa a karamar hukumar Zurmi an yi kansilan riko har 19, inda karamar hukumar take da Mazabu 11. Hakama karamar hukumar Maradun anyi Kansilolin riko har 11 maimakon 10.

Bisa wannan ne ya kalubalanci Gwamnatin PDP a kan ta bayyana inda ta samu goyon bayan dokar kasa kan yin wannan aika-aikar.

Idan har ba’a kalubalanci wannan aika-aikar ba, akwai yuyuwar nan gaba, sai PDP ta cire zababben dan Majalisar dokoki  ta kawo na rikon kwarya. A cewarsa.

A bayaninin baiyana ko za su je kutu ne su kalubalanci wannan lamarin da gwamna ya aiwatar wanda suke ganin karara babu adalci a cikinsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *