Spread the love

 
Daga Ismail Sani Yabo

 Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta ware wani kaso don tallafawa jama’a, talakawa maras karfi a cikin al’umma, da ya Shafi abinci shinkafa da man girki. 


A jihar Sakkwato gwamnatin jihar a karkashin  kwamishinan lafiya  Dakta Muhammad Ali Inname ya bayar da amanar rarraba tallafin ga hukumar Zakka da Wakafi ta jiha Wadda Malam Muhammad Lawal Maidoki ke jagoranta. 

 
Domin bibiyar yanda aka yi rabon a wasu kananan hukumomi wani Dan kishin jiha  ya ziyarci kananan hukumomi uku da suka hada da Shagari, Yabo da Bodinga inda ya ganewa idonsa yadda rabon ya kai ga wadanda aka yi yarjejeniyar baiwa, tallafin tsofaffi da shekarunsu suka haura sittin da kuma mata iyayen marayu.

Kayan rabon dai ya kunshi kilogram ashirin na shinkafa hade da  galam  na mai ga kowane mutun daya, kimanin mutane 100 suke amfanuwa a kowace gunduma.
Rabon kayan an yi shi a gaban kananan hakimmai da babban basareke, haka a gaban Shugaban hukumar Zakka da wakafi da ma’aikatansa, akwai hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC da hukumar ICPC da ta Da’ar Ma’aikata Code Of Condon Berue da wakilan kare hakkin Dan’adam da ‘yan Jarida da sauransu.


Duk wadannan kungiyoyi an Samar da su ne domin su ganewa idonsu kalar wainar da ake toyawa a wurin rarrabar.
Bayan  bayar da tallafin ga jama’a, Shugaban hukumar kan tashi yayi bayani adadin abinda aka bayar da yadda ya raba; haka yana bada shawara ga wadanda suka amfana ta yadda za su yi amfanin da abin don dorewar albarka.


Shugaban ya sami yabo ga sarakunan gargajiya yadda hukumarsa ke kulasu lokaci bayan lokaci.


Haka suma wadanda suka amfana sun ci gaba da godiya da fatar alhai ga hukumar Zakka da wakafi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *