Spread the love

Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR ya amince da a bude gidajen kallon kwallon kafa bisa sharadin da likitoci da gwamnati ta gindaya, na yin amfani da safar fuska da wanke hannu da kuma bada tazara.

A wata sanarwar da ta fito daga mai taimakawa Gwamnan akan yada labarai Salihu Tanko yakasai, inda ya ce Gwamna ya bada wannan izinin ne lokacin da ya gana da kungiyar masu gidajen kallo, karkashin jagorancin Sharu Inuwa Ahalan,

A nasa Jawabin Sharu Ahlan ya tabbatarwa da gwamna cewa sun yi alkwarin bin wannan ka’idojin da aka shinfida musu.

Sannan Gwamna ya mika musu ya mika musu gudunmawar safar fuska domin rabawa a gidajen kallo.

Gwamna Ganduje na tare da mataimakin sa Dakta Nasiru Yusuf Gawuna da Sakataren Gwamnati Alhaji Usman Alhaji da Kwamishinoni da sauran manyan jami’an Gwamnati.

Wasu na ganin in dai za a bude gidajen lokaci ya yi da za a bude makarantu domin yara su koma ga karatunsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *