Spread the love

Daga Ibrahim Hamisu, Kano.

A yau ne za’a dawo da cigaba da cin kofin Laligar kasar Safaniya, tun bayan da aka ta fi hutun annobar Korona.

Kafin tafiya hutun anyi wasanni 28, sai dai za’a cigaba da wasannin ne ba tare da yan kallo ba,

Za’a fara wasannin ne tsakanin yan hamayya, inda za’a kara tsakanin Savilla da real batis da karfe 9 na daren yau agogon Nigeriya.

Wasan kwallon kafa a kasashen Turai na da matukar muhimmanci ga tattalin arzikinsu musamman.

Dole ta sa annobar Korona da yadu a kasashen suka dakatar da wasan na kwallon kafa amma yanzu an fara gwada a dawo fagen domin cutar ta yi sauki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *