Maigirma Gwamnan jihar Sakkwato Barista Aminu Waziri Tambuwal ya rantsar da sabon shugaban ma’aikatan gwamnatin jihar Sakkwato  Alhaji  Sani Garba Shuni. 


An gudanar da bukin rantsuwar a dakin taro na Gwamnatin Sakkwato, rantsuwa ta biyo bayan murabus da tsohon shugaban ma’aikata Alhaji Buhari Bello Kware ya yi a lokacin da ya kammala shekarusa na aikin gwamnati.


Sabon Shugaban ma’aikatan ana sa ran ya fito da wasu shiraruwa da za su taimaki ma’aikatan gwamnatin jiha a fannin walwalarsu da gyaran aiki don karsashinsa ya dawo. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *