Spread the love

Gwamnatin jihar Nasarawa ta umarci shugaban Makarantar koyar da aikin kula da majinyata da Ungwan zoma ta birnin Lafiya Mr. Zari Solomon da ya dakatar da Ɗalibar Makarantar Zulaihat Ibrahim Doma na tsawon shekara guda bayan an sakata ta rubuta wasikar tuba a shafin sadarwar ta na Facebook.

Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito cewa, wannan yarinya dai daliba ce a bangaren koyan aikin Ngozoma, Laifinta Shi ne ta kalubalanci Gwamnatin jihar Nasarawa kan yadda tayi watsi da makarantar da take ciki a ranar 18 ga watan Afrilun Shekarar 2020.

An yi mata wannan hukunci ne A yau 9 ga Watan Yunin 2020, saboda faɗan gaskiya.

Wannan hukunci zai tsoratar da dalibai a wasu makarantu duk wani abu da sika gani su kama bakinsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *