Spread the love

Daga Ibrahim Hamisu, Kano.

A  Litinin, nan 8 ga watan Yuni, 2020, da yamma, Allah ya yi wa mahaifin fitaccen jarumin finafinnan Hausa Ali Nuhu rasuwa.

Mista Nuhu Poloma ya rasu a Gombe sakamakon gajeruwar  rashin lafiya da ya yi iyalinsa sun faɗa wa mujallar Fim cewa shekarun sa 79 a duniya. 

Mista Poloma tsohon ma’aikaci ne a hukumar Kwastam ta Nijeriya, sannan ya taɓa zama ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Tangale da Waja a Jihar Bauchi a ƙarƙashin jam’iyyar NPN kafin a ba Gombe jiha. 

Bugu da ƙari, ya taɓa zama shugaban jam’iyyar PDP na Jihar Gombe, cikin ‘ya’yansa akwai Kiristoci da Musulmi, shi din ba musulmi ba ne ya auri mahaifiyar Ali Nuhu, Hajiya Fatima, a Kano, Wanda dama ita ta jima da rasuwa.

Muna add’uar Allah ya ba jarumi Ali Nuhu da ‘yan’uwan sa haƙurin rashin mahaifinsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *