Daga Ibrahim Hamisu, Kano.

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta samu nasarar fito da wata dattijuwa tsohuwa mai shekaru 75 da ta fada cikin rijiya mai suna malama Zuwaira Kabir, mazauniyar unguwar Tudun Wuzirchi da ke tsakiyar birnin Kano.

Jami’in hulda da jama’a  na hukumar Alhaji Saidu Muhammad Ibrahim, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata tattauna da ya yi ga manema labarai a yau a yau Litinin a Kano,

Alhaji Saidu Muhammad Ibrahim, ya kara da cewa sun samu kiran gaggawa ne daga wani mutum Malam Musbahu Sani, mazaunin unguwar ta Tudun Wuzirchi da misalin karfe 5:45 na Asubahi inda ya sanar da hukumar cewa dattijuwar ta fada rijiya yayin da take kokarin debo ruwa, nan take hukumar ta aike da jami’anta na sashen kai daukin gaggawa.

Muhammad ya kara da cewa, jami’an hukumar sun samu nasarar ceto ta da rai inda kuma aka damka ta a hannun mahaifinta Malam Mansur Isah domin kulawa da ita.

Sannan ya shawarci al’ummar Kano da su rika rufe rijiyoyin gidajensu domin kare kansu da iyalansu daga afkawa cikin matsala.

Da yawan mutane na da wannan sakacin abin da yake haddasa wasu tsofaffi fadawa cikin hadarin fadawa cikin rijiyoyi ko wasu manyan rame na zuba ruwan wanka da wanki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *