Mine ne ya yi zafi Gwamna Matawalle ya shuka Minista Sadiya a falon saukar da baki har ta yi fushi ta bar gidan gwamnati ba tare da sun hadu ba

Daga Aminu Abdullahi Gusau.

Ana tuhumar cewa banbancin ra’ayin siyasa ne ko wani abu ne tsakanin Gwamnatin jihar Zamfara da Ministar jinkai da bayar da agajin gaggawa ta Nijeriya Hajiya Sadiya Umar Faruk abin da ya yi sanadiyar daga  rabon kayan jinkai da aka shirya gudanar wa a karamar hukumar Bungudu dake jihar ta Zamfara a yau lahadin nan.   

Ministar dai, wadda ita ma ‘yar asalin jihar Zamfara ce, ta je gidan gwamnatin ne da safiyar yau tare da ma’aikatanta domin ganin gwamna Bello Muhammad Matawalle, da zimmar sheda mashi dalilin zuwansu a jihar ta Zamfara,kan rabon kayan tallàfi, amma hakan bai samu ba.

 Hajiya Sadiya, ta zauna a wajen karbar baki na gidan gwamnati ta kwashe fiye da awa biyu tana jiran gwamna ya gana da ita, amma abin ya faskara, daga bisani tabar gidan gwamnati ba tare da ganin shi ba.

Da fitowar ta tare yan tawagarta a gidan gwamnati, sai kawai  ta nufi filin jirgi na sojan sama dake a garin na Gusau, inda jirage biyu na nan suna jiranta, ta hau jirgi ta koma Abuja ba tare da yin aikin da yakawo su ba.

Da aka tuntubi mataimaki na musamman ga ministar Alhaji Musa Zabairu,  ko yasan dalilin da yasa uwargidan ta shi ba ta ga gwamna ba, sai ya ce ba shi da hurumin yin magana game da abin da ya faru, amma yace za su ba da takardar bayan taro ga ‘yan jarida, amma har lokacin ha da wannan labarin ba su bayar ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *