An samu Karin wasu mutum 12 sun kamu da Korona a jihar Kano

Daga Ibrahim Hamisu.

Ma’aikatar lafiya ta jihar Kano ta bayyana a shafinta na Tiweta cewa a yau asabar da karfe 11:45, ta ce mutane 52 ne aka yi wa gwajin cutar Korona a jihar,

Mutum 12 daga ciki an tabbatar suna dauke da cutar, yayin da aka sallami mutane 33 bayan sun warke garas,

Sannan kuma mutum 2 sun rigamu gidan gaskiya sanadiyyar wannan annoba ta Korona Virus.

Don haka jimillar wadanda aka gwada sunkai 5,347, sai jimillar wadanda suka harbu da cutar 999, sai wadanda a halin yanzu suke da cutar 536, wadanda aka sallama kuwa sunkai 415, sai kuma wadanda suka mutu adadinsu ya kai 48.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *