Spread the love

Daga Ibrahim Hamisu.

Dan wasan da ya fi kowa jefa kwallo a raga a rukunin Firimiya ta Nigeria Mustapha Ibrahim ya ce yana jiran gayyata daga babban kocin kungiyar kwallon kafa ta Nigeriya Super Eagles wato Gernot Rohr domin ya ba da ta sa gudunmawa bugawa kasarsa ta haihuwa kwallon kafa.

Mustapha Ibrahim wanda dan asalin Maiduguri ne,  da ya ke taka leda a kulub din Filato united, ya ci  kwallaye 11 a cikin wasa 25 da ya buga, wanda daga shi wasan ne aka tafi hutun Corona,

Kwanan nan dai hukumar ta NPFL ta sabunta wa  ganet Rohr kwantaragin shekara biyu, inda ya yi alkawarin baiwa ‘yanwasa daban-daban dama da ke buga wasa a   gida Nigeriya.

Mustapha Wanda  tshon dan wasan Elkanemi warriors da Eyemba ne, ya halacci gasar kwararrun Afirka mai suna CHAN a sherar 2018.

Ya ce “Nigeriya tana da kwararrun kuma gogaggun yan wasa ni ma zan iya sa kaina a cikinsu, dama ce  mai muhimman da mai horaswa ya kamata ya baiwa yan wasanmu na gida,

 “Ina da tabbaci idan aka bani dama zan goga kafadata da yan wasan da ke bugawa a turai, nasan suna da gogewa, amma ina da tabbacin zan yi aiki tukuru don na baiwa mara da kunya”.inji Mustapha Ibrahim.

‘Yan wasan gida suna da rawar da suke iya takawa in an basu dama yakamata a rika shigowa da su domin a rika gwada su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *