Spread the love


A satin da ya gabata ne wasu mutane suka kira taron manema labarai karkashin kungiyar  ‘Coalition of concern sokoto citizen wato hadin gwuiwar kungiyoyin da suka damu da halin da Sakkwato ke ciki, suka gabatar a kan shaanin tsaro dake addabar yankin Sakkwato ta Gabbas.

Taron manema labaran ya gudana karkashin jagorancin Farfasa Nasiru Gatawa  don nuna  bacin ran mutanen kananan hukumomi 7 da suke  yankin, saboda shugaban kasa Muhammadu Buhari da Gwamna Aminu Waziri Tambuwal su dauki mataki kan lamarin. 

A cikin abin da ya sanarwa manema labarai ya ce Mahara suna damuwar yankin Sakkwata to gabas da ya kunshi kananan hukumomin Gada, Gwadabawa, Illela, Sabon Birni, Isah, Wurno da Rabah dukkan wadan nan kananan hukumomin wani yanki daga cikinsu yana karkashin kulawar maharan dake cin karensu ba babbaka sun gurgunta rayuwa da tattalin arzikin yankin abin da ya yi sanadin rasa rayukkan dimbin jama’a da dukiyoyin biliyoyin naira a yankin.

Farfesa ya kara da cewar Karamar hukumar da tafi shan wuya a cikinsu ita ce Sabon Birni da maharan ke yin yadda suke so a zangon farko na shekarar 2020 sun kai hari sama 20 a karamar hukumar kawai, a farmakin da suke kai sun kashe yara da uwayensu maza sun yi wa mata fyade tare da tafiya da ‘yan uwansu domin neman kudin fansa ga mutanen kauyen. A mazaba 11 dake sabon birni kowace mazaba akwai wani gefe da maharan suka mamaye, mutane na cikin tsoron gudanar da bukin aure ko suna ko zuwa kasuwa a ranar cin kasuwa.

Wannan maganar ce kamfanin jarida na Daily Trust ya buga a labarinta, kuma hakan ya janyo hankalin maigirma Gwamna Tambuwal abin da ya sanarwa al’umma a lokacin da yake jawabi wajen kaddamar da motocin sintiri  da gwamnatinsa za ta baiwa hukumomin tsaron jihar don yakar ‘yan ta’ddar da suka addabi mutane, ya ce “Bayan na Karanta labarin na kira Daraktan DSS na Sakkwato a lokacin ina kan hanyar zuwa Abuja wajen ganawa da Shugaban kasa Muhammadu Buhari don yi masa bayani akan halin da Sakkwato take ciki, bayan Daraktan DSS ya daga Waya na Tambaye shi. Shin ko akwai wani kauye ko gari daya da ‘yan ta’adda ke rike da shi a Sakkwato? Sai Daraktan Ya ce iya saninsa da kuma bayanan sirri da yake da babu. Sai na ce masa ko ya karanta labarin da Daily Trust ta buga akai ? Ya ce a’a sai nace zan umurci daya daga cikin maaikatansa dake aiki dani, ya aika masa labarin kuma ina son a gayyato Farfesa Gatawa don ya taimaka ma gwamnati da sunayen kauyukan da garuruwan da suka fada, a taron su na ‘yan jarida don a samu a kubutar da su, bayan sun gayyato  Gatawa sai labarin ya canja ya ce shi wallahi bai san kauyukkan ba, kawai an sa shi ya karanta matsayar ne don haka don Allah ayi hakuri. Nace a kawo min shi gabana bayan na dawo Abuja don ya tabbatar da abun da ya fada a gaban jami’an DSS, kuma a hada shi da ‘yan sanda da ‘yan jarida aje duk kauyen da suka fada cewa ‘yan ta’adda ke mulki ba’a daurin aure da  zanen suna, ba’a cin kasuwa sai sun bada dama, a yi hira da mutanen garin. Aji in gaskiya ko a’a. Amma hakan bai faru ba sai ya zo ya sake maimaita abun da ya fada. Na ce to kunje kun tara mutane kun sheda masu karya maras Sheda kuma na tabbata mafi yawancin wadanda suka zo taron ba su san inda kauyukkan da suka fada suke ba, amma gashi sun bata ma Jihar Sakkwato suna kawai saboda wadanda suka aiko su ba su kaunar Aminu Waziri Tambuwal.” A cewar Gwamna. 

Farfesa Nasiru Gatawa kan maganar ya ce “Gaskiya bayanin  karanta shi kawai na yi wallahi ba ni na rubuta ba, amma dai akwai  abubuwa ko ba ka rubuta ba kana ganin suna faruwa kwana daya bayan na karanta bayanin sai da aka kai mana hari a garinmu Gatawa daya daga cikin wanda aka harba yau(Alhamis) ya rasu abubuwa ne dake faruwa, akwai san da aka ce garin Asha banza sai da ya  kai ‘yan sa kai(‘Yan banga) ne ke kula da garinsu. Amma duk abin da yake  batawa cuta ma gwamnati bana cikin shi” a cewarsa.

Farfesa ya ce su Dakta Mansur da Dakta Bashir Acida ne suka rubuta bayanin da ya karanta kan haka aka tuntubi Dakta Bashir Acida kan mi zai ce ga lamarin, “Ba maganar Farfesa na jami’a ba wanda ya kare Sikandare ana kiransa kawai a ba shi jawabi kawai bai duba ya aminta da abin da yake ciki ba ya karanta? Bai yiwuwa a ce Farfesa bai san abin da ke ciki ba ya karanta, abubuwa ne da siyasa ke son ta shigo ciki. Mu duk abin da ke ciki mun aminta da shi mun tsaya kansa.” a cewar Dakta Bashir Acida.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *