Spread the love

Daga Ibrahim Hamisu, Kano.

Jarumar masanantar shirya finafinnai ta Kannywood Mansura Isah ta bayyana bacin ranta dangane da jita-jitar da ake yadawa na cewa ta yi hadari kuma ta ma mutu.

Jarumar ta bayyana haka ne a wani faifan Vidiyo da ta wallafa ta shafinta na Instagram, inda ta sanarwa masoya da magoya bayanta cewa; Labarin ba gaskiya ba ne, karya ce kawai aka kirkira.

Mansura wace mata ce da shahararren dan wasan Kannywood Sani Musa Danja, tana cikin ‘yan fim da ke da Gidauniyar tallafawa mabukata a Nigeriya.

Mansura a lokacin da take wasan Hausa ta yi tashe sosai domin ta kasance gwanar rawa da iya shiri ga abin da ake son ta yi.

A yanzu da take da gidauniyar tallafawa marayu da mabukata tana cikin masu kokari sosai ga talafawa jama’a dake Arewacin Nijeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *