Spread the love

Daga Ibrahim Hamisu.

Masana ilmin zamantakewar Dan Adam sun yi ittifakin cewa za’a samu yalwar ‘ya’ya da yawansu ya kai Miliyan biyar a watanni shida zuwa bakwai masu zuwa a Nigeriya, sakamakon wannan zama na Lockdown.

Musa Abdullahi Sufi Wanda masanin halayyar dan Adam ne kuma mai sharhi a alamuran yau da kullum ya bayyana haka a wata da aka yi da shi a cikin shirin Radiyo mai suna Rayuwa da Korona inda ya ce “wannan zaman lockdown wato zaman gida dole yana da abubuwa da dama da yake bijirowa da su, daya daga ciki shi ne yadda ma’aurata suke samun lokaci, a wani lokaci abin da ba’a shirya masa yakan auku, misali shi ne samun juna biyu wata kila ma a lokacin ba ta gama yaye yaron ba kila yaron ma bai gama samun ingattaciyar lafiya ba, ita ma lafiyarta ba ta gama zama ingantacciya ba.

Sufi ya kara da cewa, ”shi ya sa a wannanan lokaci a keso su maaurata su kula da wannan bangare na da samar da tazarar haihuwa, domin samun ingantacciyar lafiyar uwa da jiririnta, da kuma gida gaba daya, domin uwa mai ingattaciyar lafiya ita ce ke samun lokacin da ta ke kula da gidan da mai gidan da ‘yayan ta da tsabtace gidan da muhallinta, musamman a irin wannan lokaci,

Da haka ne mace za ta samu karfin kula da tarbiyya da tsafta kamar yadda ya kamata.

Magidanta sun zauna a gida tare da matansu abin da ake ganin za su rika bukatarsu akai akai Wanda hakan zai haifar da samun juna biyun da za a haifi wadan nan yaran saboda dokar hana kulle.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *