Spread the love

“Ku barmu a Funtua ko akan titi mu kwana” In ji yan gudun hijirar Faskari ta jihar Katsina.

Dandazon ‘yan gudun hijirar da ‘Yan bindiga suka tarwatsa daga kauyukan Karamar Hukumar Faskari wadanda suka shigo Funtua sun roki hukumomi da su bar su a Funtua kar su mayar da su Faskari saboda yanayin tsaro a Faskarin bai inganta ba.

Kwanaki biyar da suka gabata ne dai ‘yan gudun hijirar suka yi sansani a makarantar firamare ta Karofi da ke cikin garin Funtua mazansu da mata, tsofaffi da kanan yara.

Labari ya bazu a cikin garin na Funtua har al’umma sun fara kai masu tallafin kayan abinci da sutura, kwatsam mahukunta su ka zo su ka ce su bar makarantar su koma Faskari a cewarsu.

Wannan sanarwa ba tai masu dadi ba ganin yadda suka baro kauyukansu kuma suka baro garin na Faskari cikin fargaba da rashin tsaro da cunkoso a sansanin na Faskarin gashi kuma mata biyu daga cikin ‘yan Gudun hijirar sun haihu a sansanin daya ma tagwaye ta Haifa.

Jaridar Taskar labarai ta ruwaito cewa, Yanzu haka ‘yan gudun hijirar sun fantsama cikin gari, wasu a masallatai don neman masauki ganin cewa ga hadari gami da iska mai karfi ta taso ana sa ran ruwan sama a daidai lokacin da aka basu umurnin fita daga harabar makarantar.

‘Yan gudun hijira a wasu jihohin Arewa suna fama da matsin rayuwa da takura da rashin kulawa abin da yakamata gwamnoni su dubi halin da suke ciki don agaza ma rayuwarsu.

Mahara sun tarwatsa mutane a kauyukka da wasu biranen Arewa in da aka samu dimbin hasarar rayuwa da dukiyoyin jama’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *