Spread the love

Daga Ibrahim Hamisu.

Mataimakin gwamnan jihar Bauchi, Baba Tela ya kamu da cutar COVID-19 wadda aka fi sani da korona.

Babban mai taimakawa gwamnan Bauchi a fanin yada labarai, Mukhtar Gidado ne ya sanar da hakan cikin sanarwar da ya raba wa manema labarai a Bauchi a ranar Laraba. Ya ce an tabbatar da hakan ne bayan gwajin da Hukumar NCDC ta yi masa sakamakon alamomin cutar da suka bayyana a jikinsa.

Baba Tela wanda shi ne shugaban kwamitin yaki da Korona da Zazzabin Lassa tuni ya killace kansa kamar yadda jaridar ‘The Punch’ ta ruwaito a jihar Bauchi.

Gidado ya ce “Ana sanar da alumma cewa mai girma Sanata Baba Tela, mataimakin gwamnan jihar Bauchi kuma shugaban kwamitin yaki da COVID-19 ya kamu da corona virus.

“Ya kamu da cutar ne a lokacin da ya ke gudanar da aikinsa na jagorancin kwamitin yaki da cutar. “Saboda haka, mai girma, Baba Tela ya killace kansa a Bauchi kuma kwararrun maaikatan lafiya suna bashi kulawa.

“Hadimin gwamnan ya ce Hukumar NCDC ta dauki samfuri daga dukkan hadimansa na kusa da suke hulda kuma an bukaci su killace kansu yayin da suke dakon sakamakon gwajin.

Ya ce gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya roki mutane su taya mataimakinsa da sauran wadanda ke fama da cutar da addu’ar samun waraka cikin kankanin lokaci.”

Sannan Gwamnan ya yi kira jama’a da su cigaba da bin shawarwarin likitoci don dakile yaduwar wannan mugungar cuta ta Corona.

Jihar Bauchi na daga cikin jihohi a Arewa da cutar Korona ke yawatawa a tsakanin mutane sai dai lamarin bai yi wani kamari na fitar hankali ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *