Spread the love

Daga Ibrahim Hamisu.

Babbar kotun tarayya dake zamanta a birnin tarayya Abuja ta yi watsi da karar tuhumar zargin almundahanar N1.1biliyan da hukumar ICPC ta shigar kan tsohon shugaban hukumar kwastam, Abdullahi Dikko Inde.

Hukumar yaki da rashawar ta shigar da Dikko Inde ne da wasu abokan harkallarsa guda biyu ne a shekarar 2019.

Da ta ke yanke hukunci Alkalanya Ijeaoma Ojukwu, a hukuncin da ta yanke ranar Laraba, ta yi watsi da lamarin saboda karar mai lamba FHC/ABJ/CR/21/2019 da lauyan ICPC, E.A Sogunle, ya shigar na janye tuhumar.

Sogunle ya bayyanawa kotun cewa duk da cewa ana neman Dikko Inde ruwa a jallo saboda yaki halartan zaman kotu, hukumar ta gaza kama shi har yanzu, saboda haka hukumar ta janye.

Wannan hukunci ya zo wa mutane ba za ta ganin yanda aka zuba ido ana jiran hukuma ta kamo Wanda ake tuhumar da ya ki zuwa gaban kotu, sai gashi ya yi nasara duk da bai taba halartar kotu kamar yadda aka bukata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *