Spread the love

Muhammad M. Nasir

Jam’iyar PDP a jihar Sakkwato ta mayar martani ga jamiiyar APC kan takardar da fitar na kalubalantar gwamnati Aminu Waziri Tambuwal ba ta aiwatar da komai ba a cikin shekarru biyar, abin da jam’iyar PDP ta musanata a wata takarda da aka rabawa manema labarai a jihar Sakkwato wadda shugaban jam’iyar Alhaji Ibrahim Milgoma ya sanyawa hannu.

 Milgoma ya ce Tambuwai Ya tsabtace fanin sha’anin kudi da ke cike da manyan beraye. in da ya gano ma’aikatan bugi da wasu manyan APC ke amfana da su, wanda hakan ya sanya gwamnatin jiha samun rarar Miliyoyin Nairorin jama’a daga hannun su don biyan bukatar kansu.

“Ya samar da sabon tsarin zamani na tattara haraji wanda ya samu karbuwa a ciki da wajen jiha. Inda ya soma seta tattalin arzikin jiha da manyan berayen APC suka lalata. In da hakan ya bashi damar samar da kudade Naira Biliyan 4 don tallafawa jama’a masu karamin karfi da kudi Naira dubu 20 kowannensu, a dukkan fadin kananan hukumomin 23 na jiha don soma kananan kasuwanci. Hakama Gwamna ya gina sabon Bankin Micro finance don samar da bashi mai sauki ga Jamaar jihar Sakkwato, in da shi ma aka ware Naira Biliyan 2, tuni suka shiga hannun Mutane.” a cewar shugaban jam’iya.

Da ya jiuya kan ‘yan adawarsu magoya bayan jam’iyar APC ya ce ba su san darajar rayuwar mutane ba ne har suke kurarin gwamna bai yi jawabi kan cikarsa shekara daya a wa’adi na biyu ba.  

“A lokacin da sauran takwarorin sa ke cikin bukukuwan Murnar cika Shekara daya a karo na biyu na mulkin su, wato shekaru biyar (5) kenan a jumla ce, shi kuma Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya tsinci kansa a wani yanayi wanda yasa dole ya kama hanya zuwa Abuja don magance matsalar. ”      

“Babban gurin sa shi ne ganawa da Shugaban kasa Muhammadu Buhari don sanar da shi irin yadda yan bindiga da masu satar mutane, ke cin karen su ba babbaka da rayukan mutane da dukiyoyin su a karamar hukumar Sabon Birni dake Sakkwato.”

 “Saboda  rashin ganin  darajja rayuwar Jama’a, a wurin shugaban jam’iyar APC  na Sakkwato yana son kowa ya yi biris da iftala’in da Sabon Birni da sauran kananan hukumomi a Sakkwato suka shiga, sun maida hankalin su ga jawabin da Maigirma Gwamna Aminu Waziri Tambuwal zai yi na irin dimbin ayukkan da aka yi a kowane sako da lungu na jihar Sakkwato wanda su ‘yan adawar suka zamo makafi a kai.” kalaman shugaban jamiya ne.

  Ya ce duk da kulle-kulle da Zagon kasa da APC ke cigaba da yi wa Maigirma Gwamna Tambuwal, har yanzu Gwamna bai yi kasa a gwuiwa ba, wajen sauke nauyin da Allah ya aza masa na jagorancin jihar Sakkwato.  

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *