Spread the love

Daga Comr Abba Sani Pantami.

Gwamnatin Tarayya ta umarci ma’aikatan ta daga mataki na 14 zuwa sama, da su ci gaba da aiki a kowacce rana daga ranar Talata, 2 ga Yuni, 2020.

Shugaban ma’aikatan farar hula na tarayya, Dakta Folasade Yemi Esan ce ta sanar da hakan a cikin wata sanarwa da daraktan yada labarai, Mrs Olawunmi Ogunmosunle, ta sanya wa hannu ranar Talata a Abuja.

Don haka ana umurtar duk kannin ma’aikatan gwamnatin da su koma wajan aiki, domin cigaba da aiki kamar yadda suka saba kullun; Litinin zuwa Juma’a daga karfe 9:00am zuwa karfe 2:00pm na rana a kullum.

An kuma umurci jami’an da su tabbatar sunbi dokokin wajan bin umurnin hukumomin lafiya, domin kaucewa kamuwa daga cutar Corona.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *