Spread the love

Daga Ibrahim Hamisu.

Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da shawarar kwamitin kar ta kwana na fadar shugaban kasa kan cutar COVID-19 PTF na sassauta dokokin da aka kafa a jahohin Legas da Abuja da Ogun da jihar Kano, domin takaita yaduwar cutar, za a daina zirga-zirrga a jihohin daga karfe 10 na dare zuwa 4 na safe daga gobe Talata a kullum.

Shugaban kwamitin wanda shi ne sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ya sanar da cewa an sun gana da shugaba Buhari kuma sun bashi shawara kan matakin da za’a dauka gaba.

Bayan ganawar, Shugaban kasa ya amince da bude wuraren Ibada (Masallatai da Majami’u kadai) da kasuwanni da Bankuna a fadin tarayya amma da sharadin za a bi dokokin da hukumar NCDC ta gindaya.

Ya ce: “PTF ta mika shawarinta kuma shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannu a aiwatar da su cikin makonni hudu masu zuwa fari daga ranar 2 zuwa 29 ga watan Yuni, 2020.”

“An sassauta dokar hana taruwa a wuraren Ibada bisa ga sharudan da PTF ta gindaya da kuma yardar gwamnatocin jihohi.”

“Za’a amince a rika shiga kasuwanni da wuraren tattalin arziki amma da lura saboda takaita yaduwar

Alummar jihar Kano dai na dakon jawabin Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Ganduje don jin yadda tsarin zai gudana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *