Spread the love

Daga Ibrahim Hamisu.

Gwamnatin tarayya ta rage farashin litar mai a fadin Nijeriya zuwa N121.50 sabanin N125.00 da ake sayarwa yanzu.

Hukumar kula da farashin man fetur PPPRA ta yi sanarwa ne a wasikar da ta aikewa yan kasuwar mai ranar Lahadi, 31 ga Mayu, 2020.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an rage farashin man fetur din ne sakamakon faduwar farashin danyen man fetur a kasuwar duniya da annobar COVID-19 ta haifar.

Wannan shine karo na uku da za’a rage farashin man fetur cikin wanann shekarar ta 2020.

A ranar 18 ga Maris, gwamnatin tarayya ta sanar da ragin farashin litar mai daga N145 zuwa N125. Daga baya a ranar 31 ga Maris an sanar da karin ragi daga N123.50 zuwa N125.00.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *