Spread the love

Muhammad M. Nasir.

Gwamnatin Aminu Waziri Tambuwal ta kasa aiwatar da aikin a zo a gani tsawon shekara biyar abin da ya haifar da wasu magoya bayan jam’iyar PDP a jihar Sakkwato dawo daga rakiyar tafiyar a jiha domin gwamnatin ta kasa samar da walwala ta romon dimukuradiyya ga magoya bayanta, ba a maganar Sakkwatawa gaba daya.  

Shugaban jam’iyar APC Alhaji Isah Sadik Acida ne ya furta kalaman a wata takarda da jam’iyar ta fitar aka rabawa manema labarai a Sakkwato, ya ce sun saba da in gwamnatin da ta cika watanni goma sha biyu takan yi bayanin abin da ta yi domin a gani a Kasa, to amma a Jihar Sakkwato, gwamnati ta yi gum da bakinta kamar Mallam ya ci shirwa. “Duk da haka dai bamu mamaki ba, saboda sabanin sauran jihohi, Jihar Sakkwato kan babu abin a zo a gani na romuwar dimokradiyya.” a cewarsa

Ya kara da cewar akwai yiyuwar gwamnatin Sakkwato ta labe bayan matsalar annobar murar mashako ta Korona a matsayin uzurin rasa samub wani aikin ci gaban Al’umma. “A Fili take Cutar Coronavirus ta bayyana a Jihar Sakkwato a watan uku na wannan shekarar ta 2020 sannan duk Gwamnan da ke son kawo wani aikin ci gaban Jama’a ya Riga ya Gama shi.”

“Tun lokacin zaben Gwamna Aminu Waziri Tambuwal a Jihar Sakkwato Mai cike da sarkakiya, Gwamnatin Sakkwato ta Kasa aiwatar da ko tsara wani aikin Raya Al’umma domin samun fitar da Sakkwato cikin kangin talauci a wannan Jihar, hakan ya sanya hukumar  kula da kididdiga ta Kasa ta bayyana cewa Sakkwato ita ce ta farko ga jeren jihohin kasar nan da suka fi talauci.” in ji shi 

Ya ce abin da kawai aka sani ga Gwamnatin Sakkwato shi ne, “Za mu yi”. alkawarin da bai karewa kuma ya zama gafara sa bamu ga kaho ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *