Spread the love

Sabuwar rigima ta barke tsakanin gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-rufa’i da jagoran jam’iyar APC na kasa Sanata Asiwaju Bola Tinubu, Gwamnan Kadunan ya ce ba ruwansa da Tinubu.

El-rufa’i ya bayyana yana da wata jikakkiya tsakaninsa da jagoran a lokacin da yake taya ministan tsaron cikin gida tsohon gwamnan Osun Rauf Aregbesola murnar cikarsa shekara 63 da haihuwa, ya nuna tsohon gwamnan mutuminsa ne amma Tinubu bana sa ba ne suna da bambancin ra’ayi.

Wannan kalami ya fito da rashin jituwar da ke tsakaninsu da aka dade ana yada jita-jitar. Dukkansu jigo ne a jam’iyar APC ana hasashen dukkansu na sotsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023.

Wasu na ganin jam’iyar APC wannan rikinin in ba ta yi da gaske ba yana iya raba ta gida biyu abin da zai iya sanyawa ta tarwatse gaba daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *