Spread the love

Na so ace lokacin da Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto yaje fadar Shugaban kasa, yayi koyi da irin Abin da Gwamna Babajide Sanya-Olu na jihar Legas yayi.

Lokacin da aka yi gobara ta kama wata makaranta sanadiyar bindigar da wata tankar Mai ta yi, inda mutane da dama suka mutu, abin ya girgiza duk wanda ya kalli guraren da abin ya auku.

Da Gwamna Sanya-Olu yaje fadar shugaban ƙasa don yi masa bayani kan abin da ya auku sai da ya tafi masa da hotunan tashin hankali na abin da ya faru, domin shugaban ƙasa ya gani yaga irin girman al’amarin, wanda ko shakka babu abin ya kaɗa zukatan shugaban ƙasa.

Irin misalin Abin da Sanyo-Olu yayi, na so ace Gwamna Tambuwal yayi, a lokacin da zai gana da shugaban kasa kan halin da ake ciki a Sabon Birni na jihar Sokoto.

Irin munanan hotunan tashin hankali na gawarwaki da suka cika soshiyal mediya da kuma yadda aka dinga sanyawa gidajen mutane wuta, duk ya kamata ace Gwamna ya kaiwa Shugaban kasa wadannan hotuna an nuno shi yana kallonsu yana jimami.

Watakila, wannan zai sanya a dauki matakin da ya dace cikin gaggawa a wannan yanki. Domin na Lura a yiwa shugaban kasa bayani da baki cewar an kashe, an kone, an mutu… duk wani Abu ne da ya saba ji.

Amma a kai masa hotunan tashin hankali masu tsuma zukata, shi ne Abinda yafi dacewa a wannan zamanin na daukar hoto. Da yake shi Sanya-Olu ya fahimci haka, shi yasa yasan yadda zai tunkari shugaban kasa ba hannu rabbana ba.

Muna rokon Allah ya kawo mana karshen wannan kashe kashe na rashin Imani da rashin tsoron Allah. Mutanan Sabon Birni da jihar Sokoto hakika muna jin zafin Abinda ke faruwa a yankinku, fatanmu hukumomi suyi duk Abinda ya dace domin kawo karshen wannan lamarin, idan kuma makirci ne wasu makiya Allah suka shirya, to, Allah ya sansu, muna fatan ya mayar musu da aniyarsu. Allah ya bamu zaman lafiya a yankinmu da kasarmu baki daya.

Ra’ayi: Yasir Ramadan Gwale

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *