‘Yan sanda a zamfara sun cafke mutane 251, kan ƙin bin dokar hana haƙon zinari

Daga Aminu Abdullahi Gusau.

Rundunar ‘yan sandan jihar zamfara yau ta baje kolin mutane dari biyu da hamsin da ɗaya, wayanda ake zargi da ƙin bin doka da gwamnatin tarayya ta sanya ta hana hakon zinari a duk fadin jihar.

Da yake jawabi ga manema labarai, kwamishinan yan sandan jihar, CP Usman Nagogo, yace, sanin kowane gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayar da dokar dakatar da hakon zinari.

Ya kara da cewa, a shekarar data gabata ne aka sa wannan dokar, lokacin da ana fama da hare hare na yan bindiga, da masu satar shanu, kuma masu garkuwa da mutane don neman kudin fansa, duk a cikin wannan jihar ta Zamfara.

Kwamishinan yan sandan yace, bisa ga rahotanni da suke samu a jihar ta Zamfara ne, yasa gwamnati tarayya ta gano cewar, akwai alaka tsakanin yan bindiga dadi da kuma mahaka zinari.

“Bayanan sirri wayanda ke a hannu mu, da kuma sauran takwarorin mu dake aikin samar da tsaro, ya nuna cewa wayansu marassa kishin kasa, sun hada kai da wayanda ba yan kasa ba, suna gudanar da hakon zinari ta haram tacciyar hanya” inji shi.

CP Na gogo yace, a ranar 20/4 /2020, shi da kansa ya jagoranci, jami’an sa zuwa daya daga cikin wuraren da ake yin wannan haram tacciyar sana’a, a kauyen Kwalli dake a karamar hukumar Bukkuyum, inda suka cafke ‘yan kasar Chana biyu, tare da abokan harkar su ‘yan Najeriya. Kuma har an bada su a sashen bincike dake babbar hedikwatar yan sanda dake Abuja.

Wannan kamun na ‘yan kasar ta Chana yayi sanadiyar shugabannin tsaro na soja da yan sanda, ba da wata doka mai karfi, na cewa jami’an su su tabbatar da cewa sun bi lungu da sako na wannan kasar, sun kamo duk wanda aka samu hana hakon zinari bada izini ba.

“Biyowa bayan wannan umurnin, a ranar 21/5/ 2020, Kwamandan Brigade ta daya dake nan Gusau, Brigadier General O. M Bello, ya jagoran ci jami’an tsaro da suka hada da yan sanda ,hukumar DSS, da kuma sojoji, inda suka tarwatsa wuraren da ake wannan hakon zinari ba bisa ka’idaba dake kananan huku momin Anka, Bukkuyum da kuma Gummi”.

“Wannan aikin da akayi na tarwatsa wuraren da ake wannan hakon zinari kamar su Kawaye, Zugu, Dan Kamfani, Bagega, Dareta da kuma Daki Takwas, duk a cikin wayan nan kana nan hukumonmi yasa anyi nasarar kama masu laifi har su 250, Hadi da dan kasar Burkina faso data.”a cewar kwamishina.

A yayin wannan samamen, an samu kayan aiki gare su, da suka hada da, Injimin jawo ruwa guda (12), da mashin (29), da wasu sina dari nayin gyaran zinari, da dai sauran su, haka ma dukkan wayanda ake zargin sun amsa lafin su, kuma nan gaba kadan za’a gurfanar dasu a gaban kotu manta sabo.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *