Spread the love

Tsohon Shugaban Kamfanin Mai na Kasa a Najeriya, NNPC Maikanti Kacalla Baru ya rasu.

Wata majiya daga iyalinsa ta tabbatar wa BBC rasuwar tsohon shugaban na NNPC.

Shi ma shugaban kamfanin NNPC, Mele Kyari, ya tabbatar da rasuwar mutumin da ya gada, a wani sakon ta’aziyya da ya wallafa a shafinsa na Twitter.

An haifi marigayin a garin Misau na jihar Bauchi da ke arewacin Najeriya a 1959 kuma ya halarci Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria 1982 inda ya yi karatu a fannin Injiniya.

Ya soma aiki a babban kamfanin man na Najeriya a 1991 inda ya yi ta samu karin girma har ya kai ga zama shugaban na NNPC.

Maikanti Kacalla Baru ya rike mukamin shugaban NNPC daga 2016 zuwa 2019 bayan ya yi aiki a sassa daban-daban na bangaren mai a Najeriya.

Shi ne shugaban NNPC na goma sha takwas.

Ya bar mata biyu da ‘ya’ya da dama.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *