Spread the love

Daga Ibrahim Hamisu.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Mai sharia Monica Bolna’an Dongban-Mensem a matsayin mukaddashiyar shugabar kotun daukaka kara ta Najeriya.

Kakakin shugaban kasa Garba Shehu ne ya bayyana haka cikin sanarwar da ya fitar a ranar Juma’a, 29 ga watan Mayu, inda yace nadin zai fara ne daga ranar 3 ga watan Yuni.

Garba Shehu yace shugaban kasa ya nada Dongban ne bisa tanadin sashi na 234(4) da (5) na kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999, kuma nadin na tsawon watanni uku ne.

Mai sharia Monica dai yar asalin karamar hukumar Shandam ce ta jihar Filato.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *